Za a bude shawarwarin shimfida zaman lafiya a tsakanin bangarori daban daban na Yemen
Manzon musamman na MDD mai kula da batun Yemen Ismail Ould Cheikh Ahmad ya bayyana cewa, bangarori daban daban da rikicin kasar Yemen ya shafa sun amince da dakatar da nuna kiyayya da juna a duk fadin kasar tun daga ranar 10 ga watan Afrilu, kana za su sake yin shawawarin shimfida zaman lafiya a kasar Kuwait a ranar 18 ga watan Afrilu, inda za su maida hankali ga janye dakaru, mika manyan makamai ga gwamnatin kasar, tabbatar da tsaro a lokacin gwamnatin wucin gadi, farfado da hukumomin kasar, yin shawarwarin sulhuntawa a fannin siyasa, kafa kwamitin musammsan kan batun sakin mutanen da ake tsare da su da sauransu. (Zainab)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku