in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jihar Bauchi za ta ci gajiya daga ziyarar gwamna Muhammadu Abukakar a nan kasar Sin
2016-04-20 20:05:19 cri

Gwamnan jihar Bauchi Muhammed Abdullahi Abubakar, ya ce jihar sa za ta ci gajiya mai tarin yawa daga ziyarar aiki da ya gudanar a nan kasar Sin. Gwamnan wanda ya lasafta wasu daga sassan da al'ummar ta Bauchi za su ci gajiya, yayin zantawar sa da wakilin mu a Larabar nan a nan birnin Beijing, ya ce kasar Sin na da aniyar ci gaba da hadin gwiwa da Najeriya a fannoni samar da ci gaba masu tarin yawa.

Daga karshe gwamna Abubakar ya bayyana kyakkyawan fatan dorewar dangantakar zumunta, da cimma moriyar juna tsakanin kasar Sin da tarayyar Najeriya. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China