Haka kuma, bisa rahoton da hukumar ta bayar, an ce, hukumar tsaron kasar ta kama wani wanda ya shirya harin, wani dan kasar Mauritania mai suna Fawwaz Ould ah-Meida, a wata unguwar dake birnin Bamako, sa'an nan, kuma an gano boma-bomai da bindigogi da dama tare da shi.
Daga bisani kuma, hukumar ta bayyana cewa, Fawwaz yana shirya wani hari na daban da zai kai a karshen makon din a birnin Bamako a yayin da aka kama shi.
A kalla mutane 20 ne suka mutu a cikin harin ta'addanci da aka kai otel Radisson Blu, ciki har da 'yan kasar Sin guda 3, an kuma harbe dakaru guda biyu wadanda suka kai hari a otel din. Kuma reshen kungiyar al-Qaeda ta yankin Maghreb ta sanar da daukar alhakin harin na Otel Radisson Blu. (Maryam)