A cewar wannan sanarwa, shugaban kasar Mali an masa tiyata, a wani asibitin birnin Paris, kan cutar makogwaro, wato kansar dake lalata wasu sassan makogwaro da kuma a fannin aikin likitanci ake iya magance ta sosai.
Abubuwan da suke biyo daga baya sun zo cikin sauki. Kuma jinya na gudana yadda ya kamata, in ji fadar shugaban kasar Mali. (Maman Ada)