Shafin Internet na ma'aikatar tsaron Faransa ya bayyana a ranar 12 ga wata cewa, motar sulken na kan hanya gaban wani ayarin motocin sojojin Faransa, yayin da ta taka bom din a birnin Tessalit, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar sojin Faransa guda nan take, tare da jikkatar wasu sojoji 3.
A cikin 'yan shekarun nan, yanayin da ake ciki a Mali ya shiga tangal-tangal, a shekarar 2013, Faransa ta tura sojoji don taimakawa gwamnatin Mali, sai kuma daga baya, M.D.D. ta fara tura sojojin kiyaye zaman lafiya a kasar Mali. A karkashin shiga tsakani da kasashen duniya suka yi, a watan Yuni na shekarar 2015, bangarorin daban daban na Mali sun kammala daddale yarjejeniyar samar da zaman lafiya. Ko da yake, yanayin da ake ciki a wurin ya tabbata, amma lokaci-lokaci, a kan samu tashe-tashen hankali.
Bisa labarin da kafofin yada labaru na Faransa suka bayar, an ce, yanzu haka Faransa tana da sojojinta 3500 a kasashe 5 dake yankin Sahel, kuma ta kafa sansanonin soji da yawa a wurin.(Bako)