Rahoton ya bayyana cewa, da karfe 7 na daren ranar 12 ga wata, wani sojan kiyaye zaman lafiya ya harbe ma'aikatan kiyaye zaman lafiya uku a sansanin, lamarin da ya haddasa rasuwar biyu daga cikinsu nan take, yayin da na ukun ya samu raunuka.
Sai dai an samu nasarar damke wanda ya kai harin, sannan ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.
A ranar 25 ga watan Fabrairu, an kaddamar da makamancin wannan harin a wani sansanin MDD dake birnin Kidal a arewa maso gabashin kasar Mali, wani sojan kasar Chadi ya harbi shugaban rundunar, lamarin da ya haddasa rasuwarsa, sannan wani jami'in aikin likita ya rasu sakamakon wannan hari. (Maryam)