in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban MDD yayi allawadai da tashen tashen hankalin zanga zanga a Kidal dake Mali
2016-04-21 09:44:23 cri
Babban sakatare na MDD, Ban Ki-moon ya yi allawadai a ranar Laraba kan tashe tashen hankali na zanga zanga da suka faru a ranar Litinin 18 ga watan Afrilu a Kidal, dake arewacin kasar Mali, wadanda suka janyo mutuwa da jikkatar mutane da dama.

A cewar wasu bayanan na farko, masu zanga zanga biyu suka mutu yayin da dama suka jikkata, in ji kakakin sakatare janar a cikin wata sanarwa.

Sakatare janar yayi allawadai da lalata kayayyakin da aka yi a filin jirgin saman Kidal, kayayyakin da ke da muhimmanci wajen gudanar da ayyuka da tallafawa al'ummomin yankin, har ma da na tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake kasar Mali (MINUSMA) in ji jami'in.

Ban Ki-moon ya aika ta'aziya ga iyalan mamatan da fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata. Ya kuma dauki niyyar tabbatar da abin da ya faru game da wadanda suka mutu da kuma jin rauni.

Sakatare janar yayi kiran gaggawa ga bangarorin da abin ya shafa da kuma jami'an cikin gida na Kidal, har ma da wakilan gungun kungiyoyin Azawad, da su bada hadin kai domin kwantar da rikici tare da kai zuciya nesa domin bada damar yin bincike kan ainihin abubuwan da suka faru. Maido da zaman lafiya da doka da oda a yankin zai taimakawa wajen tafiyar da harkokin filin jirgin Kidal da kuma bunkasa kokarin hadin gwiwa tare da tallafin yarjejeniyar zaman lafiya, a cewar kakakin.

Haka kuma, Sakatare janar ya jaddada niyyar MDD na taimakawa zaman lafiya a kasar Mali da kuma aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China