A cewar wannan sanarwa, mutum shi ne Alou Doumbia da aka sani da Man, mai shekaru kusan talatin da haifuwa, dake cikin harkokin sufuri da sayar da tsoffin motoci. Cafkewar tasa da jami'an musammun na DGSE suka yi, na cikin cigaba na bincike da gwamnatin kasar take yi bayan harin Grand Bassam, in ji wannan sanarwa.
Kome ya nuna cewa hada kai da mista Doumbia da ma sauran abokansa game da wannan lamari ya shaida wani irin ta'addanci na cikin gari. Yanzu mazauna birane suke fadawa cikin tarkon samun kudi ba tare da wahala ba, in ji wannan sanarwa ta DGSE tare da yin kira ga al'umma da su kasance cikin shiri game da wannan sabon al'amari.
Harin Grand Bassam yayi sanadiyyar mutuwar mutane 19, daga cikinsu akwai sojojin Cote d'Ivoire uku, harin kuma da kungiyar Al-Qaida dake yankin Magreb ta dauki alhakin kaiwa. (Maman Ada)