A yayin wannan rangadi nasa a arewacin kasar da Bamako, mista Lanzer ya gana da mambobin gwamnatin Mali, hukumomin yankuna da kungiyoyin fararen hula da na jin kai. Ya kuma samu damar zuwa biranen Gao da Kidal domin tattaunawa da mutanen da rikicin ya fi shafa tare da ziyartar wasu ayyukan jin kai, in ji wannan sanarwa.
Muhimman ci gaba kamar sake bude makarantu da dama, da kyautatuwar samu ruwan sha da kiwon lafiya, an samu ci gaba sosai kansu. Ci gaban komawar hukumomin gwamnati ya kasance muhimmin abin da ya kamata a tabbatar da kuma karfafa ayyukan ci gaba tare da taimakon kungiyoyin jin kai da ci gaba, in ji mista Lanzer.
A fage, kuma ya lura da kyautatuwar yanayi dalilin sake tura wani bangaren jami'ai a ma'aikatun gwamnati dake muhimmanci da ma goyon bayan kungiyoyin ba da agaji.
Amma duk da haka, wadannan ci gaba da aka samu suna jan kafa a wasu yankuna inda har yanzu ake fuskantar matsalar tsaro dake kuma kawo cikas ga ayyukan yau da kullum, lamarin dake kara tura yawancin al'ummomi cikin mawuyacin hali, in ji sanarwar. (Maman Ada)