An tsara jadawalin wasannin ne a katafaren filin wasa na Maracana a ranar Alhamis din data gabata a Rio de Janeiro, inda tawagar 'yan wasan ta nahiyar Afrika zata buga wasa da kungiyoyin wasannin na Japan daga nahiyar Asiya, da Sweden daga nahiyar turai, sai kasar Colombia daga yankin Amurka a wasannin na Rio.
Da yake jawabi daga Rio de Janeiro bayan tsara jadawalin wasannin, Siasia yace, ba za'a iya cewa kyakkyawa ko mummunan tsari ba ne jadawalin wasannin, kuma yana da kyakkyawar fatar samun nasara a rukunin wasannin da kulub din zai kara. Ya ce baya ga kasancewarta a rukinin B a gasar wasannin, yana fatar Najeriyar zata samu tsallakewa a rukunin wasannin.
Ya ce burin da yake da shi shine na samun lambar girmamawa ta zinare a wasannin na Rio, tun bayan nasarar da kasar ta taba samu na lambar girmamawa ta azurfa a gasar wasanni ta Beijing a 2008, kuma a cewarsa, idan ya koma Najeriya, zai hada kai da sauran masu ruwa da tsaki a harkar wasanni ta kasar don gudanar da shirye shiryen da suka dace, domin cimma wannan nasara.(Ahmad Fagam)