Da yake tsokaci game da hakan, kakakin hukumar wasan damben boksin na kasar ta Uganda Fred Kavuma, ya ce tawagar su, za ta koma gida daga Yaounden kasar Kamaru, bayan fafatawa da suka yi a gasar nahiyar Afirka ta Damben boksin, wadda kwamitin gasar Boksin na kasa da kasa ko AIBA ke shiryawa.
Daya daga 'yan wasan boksin na kasar ta Uganda wato Ronald Serugo, zai yi fita ta biyu ne a gasar Olymphic, bayan ya samu nasara kan abokin karawar sa daga Afirka ta Kudu wato Sikho Nqothol da maki 2 da 1, a rukunin masu matsakaicin nauyi, yayin da shi kuma Katende ya doke Moroke Mokhotho na kasar Lesotho a wasan da suka dambata.
Yanzu haka dai 'yan damben biyu za su bi sahun takwarorin su 9 daga Ugandan, domin fafatawa a gasar Olympic da Brazil za ta karbi bakunci nan gaba cikin wannan shekara.