Kafin ya sanar da hakan, Bolt ya ce kocinsa Glen Mills ya shawarce shi da ya ci gaba da halartar wasanni har zuwa shekarar 2020. Amma a nasa bangaren, dan wasan wanda ya taba samun lambobin zinariya guda 6 a wasannin Olympics, ya ce bayan da ya samu nasara a Rio, babu dalilin da zai sa shi ci gaba da halartar wasanni a matsayin koli.
Dan wasan mai shekaru 29 a duniya, ya gaya wa manema labaru cewa, ba shi da cikakkiyar niyyar sake kwashe karin shekaru 4 yana samun horo domin wannan gagarumar gasa wadda ke gudana shekaru hudu-hudu ba.
Bolt ya samu lambobin zinariya a wasannin tsere na mita 100, da mita 200, gami da gudun ba da sanda na mita 400, a wasannin Olympics na London a shekarar 2012, kana ya samu makamantan su a gasar Olympics ta birnin Beijing a shekarar 2008.
A gasar da za ta gudana a watan Agustan bana a Rio, Bolt ya ce yana sa ran kare kambinsa a wadannan wasanni, musamman ma a wasan tsere na mita 200.