in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasanni suna inganta zamantakewa, inji jami'in MDD
2016-04-07 09:37:52 cri
Sakatare janar na MDD Ban Ki-moon, ya ce wasannin motsa jiki wata kakkarfar hanya ce ta bunkasa ci gaban dan adam da samar da daidaito, da kwanciyar hankali ga dukkan jinsin bil adam.

Mista Ban ya furta hakan ne a cikin wani sakon da ya gabatar na zagayowar ranar wasanni ta MDD don bunkasa zaman lafiya wanda ake gudanarwa a duk ranar 6 ga watan Afrilu na kowace shekara.

Mista Ban, ya bayyana wasanni a matsayin hanyar dake samar da gagarumin sauyi a fannin zamantakewar al'umma.

Ya kara da cewar, wasannin na kara lafiya, da zaman lafiya, da fahimtar juna da kwanciyar hankali, sannan yana taimakawa wajen ci gaba da samar da daidaito, da samar da ayyukan yi ga mata da 'yan mata da masu bukata ta musamman, kuma babbar hanya ce ta samar da ilmi mai inganci a makarantu, da tabbatar da hadin kai.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China