'yan wasan na koci Claudio Ranieri, yanzu haka sun yi gaba da maki 8 sama da kungiyar dake biye da su wato Tottenham Hotspur, wanda ta rasa nasara a wasan ta da Bournemouth.
A wani ci gaban kuma Arsenal ta doke Everton da ci 2 da nema a filin wasa na Goodison Park, hakan ya sanya kungiyar kaucewa buga wasanni uku a jere babu nasara a gasar ta Premier. Hakan ya nuna cewa Arsenal din za ta shiga karshen mako ke nan tana matsayi na uku a teburin gasar.
A wasan Chelsea da West Ham United kuwa, kungiyoyin biyu sun tashi kunnen doki 2 da 2, wanda hakan ya baiwa Chelsea damar kare kambin ta na ci gaba da samun nasara a dukkanin wasannin da ta buga, wato dai har wannan wasa ba a samu nasara a kan ta ba.
Teburin gasar Premier dai na da Leicester a matsayi na daya da maki 66, sai Tottenham Hotspur mai maki 61, yayin da Arsenal ke matsayi na 3 da maki 55. Manchester city ce ke biye a matsayi na 4, sai west Ham da kuma Man. United a matsayi na 5 da na 6.