Yanzu Sinawa masu goyon bayan kulob din Man. United yawansu ya kai fiye da miliyan 107, adadin da ya fi na sauran kasashe duniya.
Cikin sanarwar, an ce Man. United, za ta gudanar da ziyara ta kwanaki 8, cikin ayyukan da kulob din zai yi don share fagen wasannin da zai halarta a kakar wasanni ta 2016-17 karkashin tsarin gasar Premier League. Sa'an nan kungiyar ta ce za ta sanar da karin bayani dangane da ziyarar ta ta a kasar Sin, wanda zai kunshi ranar isowa kasar ta Sin, da kungiyoyin kasar Sin da zai kara da su, da dai sauransu.
Bugu da kari sanarwar ta bayyana cewa, Man. United ya fara kai ziyara kasar Sin a shekarar 1975, daga bisani ya kai karin ziyara karo 9 zuwa kasar, inda ya taba buga kwallo tare da kuloflikan kwallon kafan kasar Sin cikin wasanni 12.
A nasa bangare, mataimakin shugaban kulob din Man. United mista Ed Woodward, ya ce kulob dinsa na da hulda mai kyau da kasar Sin, kana yana alfahari da irin dangantaka, da yadda ake samun masu sha'awar kulob din masu dimbin yawa a kasar Sin.