Wasu sabbin munanan zarge zarge sun fito dake shafar halayyar sojojin MDD dake Afrika ta Tsakiya. Na kadu sosai da jin wannan labari, kuma raina ya baci matuka game da wadannan bayanai na yin lalata kan kananan yara da dakarun MDD suka aikata a tsawon shekarun baya bayan nan, in ji mista Ban a yayin wani taron manema labarai a ranar Laraba a cibiyar MDD.
Ya bayyana cewa, ba za a rufe idanu ba ga duk wani aikin da zai tura mutane jin tsoron MDD maimakon su amince da ita, wadanda suke wa MDD aiki ya kamata su girmama dokokinta da manyan ka'idodinta, in ji Ban Ki-moon tare da bayyana cewa ya nada wani kwamiti mai zaman kansa dake kunshe da manyan jami'ai domin yin bincike kan bayanan abubuwan kunyar da suka faru a Afrika ta Tsakiya.
Haka kuma ya yi alkawarin cewa, MDD za ta yi iyakacin kokarinta domin gurfanar da wadanda suka aikata laifuffukan gaban kotu.
Bisa bukatar sakatare janar, shugaban kwamitin sulhu zai gudanar da wani zaman taro na musammun game da batun lalata kan kananan yara, wanda a cewar mista Ban ke kasancewa wata babbar annoba da kasancewar wata matsalar da ke bukatar daukar nagartattun matakai. (Maman Ada)