Cikin sanarwar da kwamitin na sulhu ya fitar, ya ce Afirka ta tsakiya ta gudanar da taron dandalin tattaunawar neman sulhu a babban birnin kasar Bangui, tsakanin ranekun 4 zuwa 11 ga watan nan, ta kuma zartas da yarjejeniyar zaman lafiya, da neman sulhu, da kuma farfadowar kasa. Kana cikin yarjejeniyar, an yi alkawarin cewa za a gudanar da babban zaben shugaban kasa, da kuma zaben majalissar dokoki ba tare da wani bata lokaci ba.
A daya hannun kuma, bangarorin da wannan batu ya shafa sun kulla yarjejeniyoyin kawar da makamai, da dakile shigar da yara kanana ayyukan soji, da kuma sakin irin wadannan rukuni na sojoji yara wadanda ake tsare da su.
Dangane da hakan, kwamitin sulhun MDD ya nuna matukar yabo, tare da maraba da sakin sojojin yara sama da su dari 3, da kungiyoyin anti-Balaka da Seleka suka yi a kwanan baya.
Bugu da kari, kwamitin sulhu na MDD ya yi kira ga bangarorin da abin ya shafa da su yi biyayya ga yarjejeniyoyin da suka kulla, su kuma goyi bayan shirin kada kuri'u kan kundin tsarin mulkin kasar cikin sauri. Ya kuma yi kira ga mahukuntan kasar da su gudanar da babban zaben shugabancin kasa, tare da na majalissar dokokin kasar ba tare da wani jinkiri ba, wato cikin watan Agustar wannan shekara kamar dai yadda aka tsara tun a baya.
A sa'i daya kuma, kwamitin ya ja hankalin gamayyar kasashen duniya, da su goyi bayan Afirka ta Tsakiya, wajen ciyar da yunkurin siyasar ta gaba.
Kasar Afirka ta Tsakiya dai ta sha fama da tashe-tashen hankula, da rikice-rikice, musamman tsakanin kungiyar anti-Balaka da kungiyar Seleka, lamarin da ya haddasa babbar matsala ga yanayin jin kai a kasa.
Bisa kididdigar da MDD ta gudanar, an ce a halin yanzu, akwai 'yan gudun hijira kimanin dubu 430 cikin kasar, yayin da kimanin dubu 450 suka tsere zuwa kasashe makwabta. (Maryam)