Sa'an nan, Mr. Ayrault ya bayyana a yayin taron manema labarai da aka yi a wannan rana cewa, kasar Faransa za ta ci gaba da nuna goyon baya ga kwamitin firaministan kasar Libya da gwamnatin hadin gwiwar al'ummomin kasar, haka kuma, tana son taimakawa gwamnati kan ayyukan horas da rundunonin sojin kasar domin warware matsalolin tsaro da kasar Libya da kasashen dake kewaye da ita suke fuskanta.
A nasa bangaren, ministan harkokin wajen Jamus Frank Walter Steinmeier ya ce, kasar Jamus tana son taimakawa Libya domin yaki da kugniyar IS da sauran kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi dake kasar. Mr.Steinmeier ya yi kira ga bangarorin kasar da su mika ikonsu ga gwamnatin hadin gwiwar al'ummomin kasar da kuma fara sauraren umurnin gwamnatin cikin hanzari. (Maryam)