Tsagin gwamnatin dake ikirarin rike da madafun iko a kasar Libya ya yi murabus a jiya Talata.
Cikin wata sanarwa, an bayyana cewa, a halin yanzu, gwamnatin ta ayyana rusa kanta da kanta. Kamar yadda sanarwar ta nuna, a yanzu haka, babu majalisar zartaswa, babu shugaban kasa, babu mataimaka, babu majalisar ministoci na tsagin gwamnatin.
Wannan mataki ya zo ne mako guda bayan tawagar gwamnatin dake samun goyon bayan MDD ta shiga babban birnin kasar Tripoli.
Sanarwar ta ce, tsagin gwamnatin ta duba girman Allah ne da kuma mutanen kasar, sannan daga yanzu duk abinda zai faru a nan gaba basu sa hannusu cikinsa.
Gwamnatin mai barin gado ta ce, ta dauki matakin yin murabus ne saboda nuna damuwa game da makomar kasar, da ceto rayukan al'ummar kasar ta Libya, da kawo karshen yaduwar makamai a tsakanin al'ummar kasar a nan gaba.
Sabuwar gwamnatin wadda Fayez Serraj ke jagoranta, ta shiga birnin Tripoli a ranar Laraba ta makon jiya, inda ta yi watsi da gwamnatin hadin kan kasa, wadda a baya aka ayyana hakan, Serraj dai ya bayyana cewar gwamnatinsa za ta shiga birnin Tripoli don kwace iko.(Ahmad)