Haka kuma, wani mamba a kwamitin ya bayyana wa kafar watsa labarai ta Xinhua cewa, tawagar musamman da MDD ta tura zuwa kasar Libya domin ba da taimako da goyon baya ga kasar, ta jagoranci taron, inda mambobin kwamitin kafa tsarin mulkin kasar Libya su 32 suka halarci taron.,kuma bayan tattaunawar da suka yi tsawon makwanni uku da suka gabata, sun cimma ra'ayi daya kan batutuwan dake shafar sunan kasar, babban birnin kasar, harshen gwamnatin kasar, da kuma matsayin mata a kasar da wasu batutuwan da a da ba a kai ga cimma matsaya guda.
Daga bisani kuma, kwamitin zai kira cikakken zaman taro a birnin Al-bayda dake gabashin kasar Libya a ran 10 ga watan nan da muke ciki, domin kada kuri'u kan daftarin sabon tsarin mulkin kasar.
Kwamitin kafa tsarin mulkin kasar Libya yana da mambobi 55, amma wasu ba su halarci taron ba, sabo da rashin amincewarsu kan wasu ayyukan dake shafar tsara daftarin tsarin mulkin kasar ta Libya.(Maryam)