A yayin ganawarsu, Zhang Dejiang ya ce, majalisar wakilan jama'ar kasar Sin tana son kara yin musaya da majalisar dokokin kasar Nijeriya a fannonin dake shafar yaki da cin hanci da shari'a da dai sauransu, domin kyautata dokokin hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya da kuma ciyar da hadin gwiwar hukumomin kafa dokoki na kasashen biyu gaba.
A nasa bangare kuma, shugaba Buhari ya ce, kasar Nijeriya za ta nuna kwazo da himma kan shirye-shiryen bunkasa kasashen Afirka guda goma da ake gudana karkashin taimakon kasar Sin, haka kuma, kasarsa tana son ci gaba da karfafa mu'amala da hadin gwiwar dake tsakanin hukumomin kafa dokoki na kasashen biyu a nan gaba. (Maryam)