in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Buhari: Akwai kyakyawar makoma game da hadin gwiwa tsakanin Sin da Najeriya
2016-04-12 15:47:37 cri

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya ce harkokin cinikayya da kasuwanci tsakanin Sin da Najeriya sun samu bunkasa matuka musamman ma a wannan karnin da muke ciki, inda jimillar kasuwanci tsakanin sassan biyu ya karu daga dalar Amurka biliyan 2.8 a shekara ta 2009, ya zuwa dala biliyan 14.9 a shekarar bara.

Shugaban wanda ya bayyana haka da safiyar Talata a nan Beiing yayin da yakehalartar taron dandalin hadin gwiwar cinikayya da zuba jari tsakanin Sin da Najeriya, ya ce a nahiyar Afirka Najeriya na cikin kasashen da ke kan gaba a fannin cinikayya da kasar Sin, hakan a cewarsa ya biyo bayan yarda, da mutunta juna, tare da kokarin cin gajiya da sassan biyu ke da shi tsawon lokaci.

A daya bangaren kuma shugaban na Najeriya, ya ce akwai wagegen gibi a fannin cin gajiya tsakanin sassan biyu, duba da cewa 'yan kasuwar Sin ne ke cin kusan kaso 80 bisa dari na gajiyar wannan cudanya, sai dai duk da hakan, ya ce wannan dandali tamkar wata dama ce ta zakulo hanyoyin rage wannan gibi.

Kaza lika shugaba Buhari ya ce yayin ganawarsa da shugaban kasar Sin Xi Jinping a bara a birnin New York, sun amince su gudanar da hadin gwiwa wajen bunkasa harkokin cinikayya, da zuba jari, da dai sauran su, duka dai domin cimma burin bunkasa tattalin arzikin Najeriya, da kuma wanzar da musaya tsakanin sassan biyu.

Daga karshe, ya bayyana wasu manyan matakai da gwamnatin Najeriya ke dauka domin inganta tsaro, musamman ma domin masu zuba jari su samu kyakkyawan yanayi na gudanar da harkokin su a Najeriya. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China