in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban tarayyar Nijeriya zai fara ziyarar aiki kasar Sin
2016-04-06 20:29:46 cri
A Larabar nan ne kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang, ya bayyana cewa shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari, zai gudanar da ziyarar aiki a nan kasar Sin, bisa goron gayyatar da takwaransa na kasar ta Sin Mr. Xi Jinping ya gabatar masa.

Mr. Lu ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai a Larabar nan, ya ce shugaba Buhari zai ziyarci kasar Sin ne tsakanin ranekun 11 zuwa 15 ga watan nan na Afirilu.

Kaza lika Mr. Lu ya bayyana cewa a bana Sin da Najeriya ke cika shekaru 45 da kulla huldar diflomasiyya. Kuma yayin ziyarar da shugaba Buhari zai gudanar, zai tattauna da shugaba Xi Jinping, da firaminista Li Keqiang, da kuma shugaban majalissar wakilan jama'ar kasar Sin Zhang Dejiang. Inda ake sa ran za su yi musayar ra'ayi game da wasu muhimman batutuwa da suka jibanci kasashen su.

Har ila yau, sassan biyu za su rattaba hannu kan yarjeniyoyin hadin gwiwa, tare da gudanar da dandalin tattaunawar hadin gwiwa a fannin samar da hajoji. Sa'an nan za su kira liyafar cikar dangantakar su shekaru 45 da kafuwa.

Buhari zai kuma ziyarci biranen Shanghai, da Guangzhou, a yayin wannan ziyara.

Daga nan sai Mr. Lu ya bayyana Najeriya a matsayin abokiyar huldar Sin ta kusa, kana sassan biyu sun dade suna gudanar da harkokin ci gaba cikin shekaru 45 da suka gabata. Ya ce akwai kyakkyawan fatan cewa ziyarar shugaba Buhari za ta bude sabuwar kofar raya dangantakar kasashen biyu yadda ya kamata.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China