in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi ganawa tsakanin shugabannin kasashen Sin da Najeriya
2016-04-12 21:40:29 cri

Yau Talata shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na Najeriya Muhammadu Buhari a babban dakin taro na jama'ar kasar Sin, inda shugabannin biyu suka tsaida kudurin yin aiki tare da nufin cigaban dangantaka da abokantaka dake tsakanin kasahen biyu bisa manyan tsare-tsare, tare da kara kawo alheri ga jama'ar kasashen biyu.

A yayin shawarwari, shugaba Xi Jinping ya nuna cewa, shekarar da muke ciki, shekaru 45 kenan cif cif da kulla huldar diplomasiyya a tsakanin Sin da Najeriya. A bisa kokarin da bangarorin biyu suka nuna, kasashen biyu sun samu manyan nasarorin ta fuskar cin moriyar juna a fannoni daban daban. A wannan yanayin da ake ciki na neman bunkasuwar tattalin arzikin duniya bai daya, da zurfafa hadin kai da sada zumunta a tsakanin kasashen biyu, sannan kuma yana amfani wajen tabbatar da zaman lafiya da zaman karko da kuma neman cigaban duniya.

A nasa bangaren, shugaba Buhari ya bayyana cewa, yana farin ciki da cika shekaru 45 da kulla huldar tsakanin kasar Sin da Najeriya, ya ce ana samun karuwar bunkasuwar dangantakar tsakanin kasashen biyu, kuma ana cigaba da zurfafa hadin kai a tsakaninsu a fannoni daban daban. Najeriya ta nuna godiya da irin tallafin da kasar Sin take ba ta wajen raya cigaban muhimman kayayyakin more rayuwa cikin dogon lokaci. Najeriya tana fatan gaggauta aiwatar da yarjejeniyoyin da kasashen biyu suka cimma, don samun moriyar juna a fannonin aikin gona, ma'adinai, da muhimman kayayyakin more rayuwa, da dai sauransu, ta yadda za a iya ciyar da bunkasuwar tattalin arzikin Najeriya ta hanyoyi da dama gaba, da inganta samar da guraban aikin yi. Ya kara da cewa, kasarsa tana fatan karfafa hadin kai tare da Sin kan harkokin kasa da kasa.

Bayan ganawarsu kuma, shugabannin kasashen biyu sun sa ido kan sanya hannu a takardun hadin kai ta fuskokin muhimman kayayyakin more rayuwa, da zuba jari, da sadarwa, da kimiyya da fasaha, da sha'anin kudi da dai sauransu. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China