in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Akwai makoma mai haske wajen inganta hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen Sin da Nijeriya
2016-04-11 10:08:43 cri
Daga ranar 11 zuwa ranar 15 ga wata, shugaban kasar Nijeriya Muhammadu Buhari zai kawo ziyarar aiki a nan kasar Sin bisa goron gayyata da takwaransa na kasar Sin Xi Jinping ya yi masa. Yayin da yake zantawa da wakilinmu kafin zuwansa, ya ce, akwai makoma mai haske wajen inganta hadin gwiwar kasashen Nijeriya da Sin ta fuskokin aikin gona, da ma'adinai, da wutar lantarki, da hanyoyin jiragen kasa da hanyoyin mota, kuma Nijeriya ba za ta wuce wannan babbar dama a cikin tarihi ba.

Shugaba Buhari ya kara da cewa, Nijeriya tana fatan karfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da zuciya guda, sabo da kasar Sin na da fasahohi, da kudi da fasahar raya tattalin arziki, haka ta nuna sahihiyar niyyar taimakawa Nijeriya, sabo da haka, Nijeriya ba za ta wuce wannan dama.

Yayin da aka tabo maganar raya dangantakar tattalin arziki da cinikayyar kasashen biyu, Buhari ya ce, gwamnatinsa ta kiyaye yarjejeniyoyin da aka daddale tsakanin kamfanonin kasar Sin da tsohuwar gwamnatin Nijeriya a bangaren hanyoyin mota, da hanyoyin jiragen kasa da tashoshin samar da wuta da ruwa. Ko da yake, Nijeriya ta kasance kasa mafi arziki a Afrika, amma ana bukatar wadannan ayyuka musamman ma ababen more rayuwa ruwa a jallo, yayin da kasar Sin ta kasance kasa ta biyu a fannin tattalin arziki a duniya, sabo da haka, Sin na da karfin daukar wannan aiki.

Buhari ya ce, a lokacin da, Nijeriya ta dogara kan man fetur fiye da kima wajen raya tattalin arziki, kana ta kashe kudade da dama wajen shigo da shinkafa da sauran amfanin gona. Nan gaba, Nijeriya za ta kashe kudade wajen raya masana'antu musamman ma ta fuskar kirkire-kirkire da sassaka, don gaggauta raya ababen more rayuwa a gida, sabo da haka, akwai makoma mai haske wajen inganta hadin gwiwar kasashen biyu.

Yayin da aka tabo maganar rashin ayyukan yi, Buhari ya ce, yanzu yawan mutanen da shekarunsu suka yi kasa da 35 ya kai kashi 62 cikin 100 a kasar, kuma mutane da dama daga cikinsu ba su da ayyukan yi. Idan aka so warware wannan matsala, hanya mafi kyau ita ce, a gaggauta raya aikin gona da ma'adinai. Kasar Sin za ta taimaka mana a wadannan fannoni. Game da raya ma'adinai, yanzu, akwai kamfanoni da dama dake hakar ma'adinai a kasar, sabo da haka akwai babbar dama wajen yalwata hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China