Wannan dai shi ne karo na farko, da aka taba samun rahoton bullar cutar a shiyyar arewa maso yammacin kasar.
Kwamishiniyar lafiya ta jahar Katsina Mariyatu Bala Usman, ta shedawa kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua cewar, tuni aka killace matashin tun bayan da aka hakikance yana dauke da kwayoyin lassa mai saurin hallaka bil adama.
A cewar jami'ar lafiyar, ana zargin matashin ya kamu da cutar ne bayan da ya kusanci gawar wani mukarrabinsa.
Mariyatu ta fada cewa, tuni aka ankarar da jami'an kiwon lafiya a dukkan cibiyoyin kiwon kafiya na jihar game da matakan da ya dace su dauka wajen tunkarar bullar cutar a dukkan yankunan kananan hukumomin jihar 34.
Kawo yanzu mutane 268 ne aka zargin sun kamu da cutar zazzabin lassa a fadin kasar, sannan mutane 138 sun mutu tun bayan bullar cutar wacce tafi kamari a watan Fabrairu.
Sai dai mahukunta Najeriya sun tashi haikan domin dakile ci gaba da yaduwar cutar. (Ahmad)