Sa'an nan, a yayin da yake ganawa tare da manzon musamman na babban magatakardan MDD kan batun Syria Staffan de Mistura, Mr. Muallem ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Syria ba za ta kaucewa halartar wannan taron ba, kana, tana tsayawa tsayin daka wajen yin shawarwarin neman sulhu ba tare da a gindaya wani sharadi ba, kuma ya kamata shawarwarin sun kasance a tsakanin 'yan kasar Syria, haka kuma, 'yan kasar za su ba da jagoranci kan taron.
Kaza lika, ya ce, al'ummomin kasar suna da ikon yanke shawara a kan makomar kasarsu, suna kuma imani cewa, za a iya kawar da kungiyoyin ta'addanci dake kasar, da suka hada da kungiyar IS, reshen kungiyar al-Qaeda na kungiyar AL-Nusra da sauransu.
Staffan de Mistura ya isa birnin Damascus a ran 10 ga wata, sa'an nan ya samu ganawa tare da Mr. Muallem a ran 11 ga wata, inda kafin ya bar kasar ya bayyana wa kafofin watsa labarai cewa, babban makasudin ziyararsa a wannan karo shi ne, tattaunawa tare da Mr. Muallem kan ayyukan shirye shiryen taron neman sulhu, haka kuma, sun tattauna kan muhimmancin yarjejeniyar tsagaita bude wuta. (Maryam)