Gidan telebijin na pan-Arab al-Mayadeen ya ruwaito kalaman mista Mekdad na cewa, kasar Syria za ta tabbatar da ikon mallaka da 'yancin kan kasar, tilas ne bangarori daban daban su girmama ra'ayin jama'ar kasar Syria.
An kammala shawarwarin shimfida zaman lafiya kan batun Syria na sabon zagaye a ranar 24 ga watan Maris na bana, a yayin shawarwarin na tsawon kwanaki kwanaki 10, gwamnatin kasar Syria da kwamitin yin shawarwari na kungiyoyin masu adawa sun cimma daidaito kan batutuwa 12. Manzon musamman na babban sakataren MDD mai kula da batun Syria Staffan de Mistura ya sanar cewa za a bude sabon zagayen shawarwarin a ranar 9 ga watan Afrilu.
Shugaban kasar Syria Bachar al Assad ya ba da umurni a watan Febrairu cewa, za a gudanar da majalisar dokokin jama'ar kasar a ranar 13 ga watan Afrilu. (Zainab)