in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar IS ta sanar da sakin mutanen Syria 300 da ta yi garkuwa da su
2016-04-09 13:58:50 cri
A jiya Jumm'a, kungiyar IS mai tsattsauran ra'ayi ta bayyana cewa, ta riga ta saki ma'aikatan kamfanin siminti na Syria guda 300 da ta yi garkuwa da su a kwanan baya.

A wannan rana, kungiyar IS ta ba da sanarwar ta kamfanin dillancin labaru na Amaq dake goyon bayanta cewa, yanzu ana ci gaba da tsare ma'aikata 20, yayin da aka kashe sauran ma'aikata 4.

Bayan yin garkuwa da ma'aikatan kamfanin siminti na Syria, an ba da labarai iri daban daban. A wannan rana, an sami labari daga sojojin Syria cewa, kungiyar IS ta riga ta saki mafi yawan ma'aikatan kamfanin a safiyar ranar 7 ga wata. Wadannan ma'aikatan 110 sun isa sansanin sojojin kasar a garin Jairod, wanda ke arewacin garin Dumeir, yayin da sauran ma'aikata 70 suka isa sansanin sojin sama a garin Dumeir. Ban da haka, dakarun kungiyar IS sun kashe ma'aikatan 6, tare da tsare wasu 30 a halin yanzu. (Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China