in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin gwamnatin Syria sun sake amshe wani birni daga hannun kungiyar IS
2016-04-04 12:43:39 cri

Rundunar sojin gwamnatin Syria ta ce dakarunta sun samu nasarar kwace birnin Gallatin dake yankin tsakiyar kasa daga ikon mayakan kungiyar IS, bayan wani bata kashi da sassan biyu suka yi.

Kamfanin dillancin labaru na kasar Syria ya bayyana cewa, sojojin gwamnatin Syria sun kai farmaki ta sama kan wasu sansanoni na dakarun kungiyar ta IS dake birnin Gallatin, kafin kuma wata tawaga ta sojojin ta kutsa kai cikin birnin. Kaza lika sojojin sun kawar da wasu boma-boman da mayakan kungiyar ta IS suka daddasa, suka kuma hallaka wasu dakarun masu yawa.

Tun dai a ranar Asabar ne sojojin gwamnatin Syria suka fara kaddamar da manyan hare-hare kan birnin Gallatin, matakin da ya basu damar cimma nasarar dakile matakan da kungiyar IS ke dauka a yammacin birnin.

A watan Agustan bara ne dai kungiyar IS ta mamaye birnin Gallatin, wanda ke tsakanin birnin Damascus fadar mulkin kasar da kuma birnin Homs, hedkwatar jihar Homs, da kuma tsohon birnin Palmyra, wanda hakan ya sanya shi zamowa birni mai matukar muhimmanci ga kasar. Tun a ranar 27 ga watan Maris ne dai sojojin gwamnatin kasar suka kwace ikon birnin Palmyra daga hannun mayakan na IS. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China