Sojojin gwamnatin Syria sun furta a jiya Jumma'a cewa, sun bude wuta kan birnin Gallatin, wani muhimmin birnin da ke yankin tsakiyar kasar Syria dake karkashin ikon kungiyar IS, domin karbe wannan birni.
Kamfanin dillancin labaru na kasar Syria ya ba da labari cewa, sojojin gwamnatin kasar sun mamaye wasu muhimman wuraren dake kewayen birnin Gallatin.
A watan Agusta na shekarar bara, kungiyar IS ta mamaye birnin Gallatin, wanda ya kasance wurin dake tsakanin birnin Damascus, babban birnin kasar da birnin Homs, hedkwatar jihar Homs da tsohon birnin Palmyra, shi ya sa, birnin yake da muhimmin matsayi sosai.
Sojojin gwamnatin kasar Syria sun kwato birnin Palmyra a ranar 27 ga watan Maris, kana sun ba da sanarwa cewa, karbe birnin na Palmyra ya karya lagon dakarun kungiyar IS sosai, a nan gaba, kungiyar IS za ta ci gaba da faduwa.(Lami)