Haka kuma, a yayin taron manema labaran da aka yi a wannan rana, Mistura ya ce, bi da bi, wakilan babban kwamitin yin shawarwari na jam'iyyar adawa ta kasar Syria za su isa birnin Geneva a ran 11 ga wata da kuma ranar 12 ga wata, kana, wakilan gwamnatin za su isa birnin Geneva a ranar 14 da ta 15 ga wata, sabo da wasu ayyukan dake shafar babban zaben kasar.
Bugu da kari, Mistura ya bayyana cewa, zai fara ganawarsa da wakilan jam'iyyar adawa a ran 13 ga wata, sa'an nan, zai gana da tawagar wakilan gwamnatin kasar Syria. Amma ganawar din ba za ta kasance yin shawarwari kai tsaye ba, sai yin musayar labarai ta bakinsa da wasu jami'an MDD a tsakanin bangarorin biyu.
Kaza lika ya ce, za a bukaci bangarorin dake shafar batun Syria da su cimma daidaito kan daftarin shirin shimfida wani tsarin siyasa na wucin gadi a kasar Syria a yayin taron shawarwarin neman sulhu da za a yi, domin fara shirin tun da wuri. (Maryam)