Kamfanin dillancin labarum kasar Syria ya ruwaito maganar shugaban lardin Homs dake tsakiya kasar na cewa, wadannan jama'a sun tashi daga Homs zuwa Palmyra da Gallatin cikin motocin safa safa sama da 40. Kafin haka dai kwararru sun riga sun isa biranen biyu, don kawar da nakiyoyin da 'yan kungiyar IS suka dasa kan hanyoyi, an kimanta cewa, za a farfado da aikin jinya, da ayyukan samar da wutar lantarki, da ruwa da dai sauransu a cikin 'yan makwanni masu zuwa.
Biranen Palmyra da Gallatin suna kudu maso gabashin birnin Homs. Kungiyar IS ta kai hari kan wadannan birane biyu a watannin Mayu da Agustan bara, hakan ya tilastawa fararen hula da dama tserewa daga gidajensu. A karshen watan Maris da farkon wannan watan, sojojin gwamnatin kasar tare da taimakon sojojin kasar Rasha sun kwato wadannan biranen biyu.
Bisa kididdigar da MDD ta yi an nuna cewa, tun bayan barkewar rikicin Syria a shekarar 2011 har zuwa yanzu, mutane dubu 250 suka rasa rayukansu, yayin da miliyan 6.5 suka rasa gidajensu. (Bilkisu)