A ran 7 ga wata, shugaban kasar Djibouti Ismail Omar Guelleh ya gana da ministan harkokin wajen Sin Mista Wang Yi a fadar shugaban kasar.
A ganawarsu, Mista Guelleh ya bayyana cewa, Sin tana kasancewa abokiyar Djibouti mai sahihanci, kasar Djibouti tana nuna godiya ga kasar Sin don zumunci da taimakon da Sin take samar mata cikin dogon lokaci. Sin ta goyi bayan Djibouti a fannonin ayyukan more rayuwar jama'a, da jigilar kayayyaki, sabo da hakan, Sin ta ba da taimako ga Djibouti wajen zama tashar ruwa da mahadar zirga-zirga a gabashin Afirka. Djibouti tana son zurfafa hadin kai da Sin bisa manyan tsare-tsare, da koyo daga wajen Sin a fannin raya tattalin arziki da zaman al'umma. Djibouti tana fatan kara samun taimako daga Sin a fannonin ayyukan more rayuwar jama'a, da kafa yankin musamman wajen raya tattalin arziki, da samar da makamashi da dai sauransu, tare da hadin kai da Sin a harkokin zaman lafiya da tsaro a gabashin Afirka.
Mista Wang Yi ya yi nuni cewa, kasar Sin tana mayar da kasar Djibouti a matsayin wata muhimmiyar abokiyar da take iya hadin kai da ita, kuma har kullum Sin tana neman raya dangantakar dake tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare kuma cikin dogon lokaci. A matsayinta na abokiya, Sin tana son zurfafa hadin kai da moriyar juna a fannonin tashar ruwa, da zirga-zirga da dai sauran fannonin da Djibouti take bukata, tana son taimakawa Djibouti domin karfafa fiffikon da take da shi, da cimma burin zirga-zirga cikin 'yanci a gabashin Afirka. Sin za ta kara karfinta wajen taimakawa Djibouti a fannonin more rayuwar jama'a, domin kara jin dadin jama'a. Bugu da kari, zurfafa hadin kai a fannin tsaro ya dace da moriyar juna, Sin tana son yin kokari tare da Djibouti domin kiyaye zaman lafiya a gabashin Afirka. (Danladi)