in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Chadi da aka tura Najeriya da Nijar za su koma gida a ranar 11 ga Disamba
2015-12-10 11:15:41 cri
Sojojin rundunar kasar Chadi da aka tura kasashen Nijeriya da Nijar, kasashe biyu dake makwabtaka da juna, domin yaki da kungiyar Boko Haram, za su koma gida a ranar Jumma'a, in ji ministan sadarwan Chadi, kuma kakakin gwamnati, Hassan Sylla Bakari a ranar Laraba.

Mista Sylla Bakari ya yi kira ga dukkan 'yan kasar Chadi baki daya da su fito kwansu da kwalkwata domin tarbon sojojin da suka kammala aikinsu. A ranar 7 ga watan Nuwamba, sojojin Chadi da aka tura a kasar Kamaru, bisa irin wannan dalili na yaki da Boko Haram, an yi musu babban tarbo a matsayin manyan jaruman kasa a birnin N'Djamena. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China