A jiya Lahadi wasu mahara 4, suka tada boma bomai a tsribirin na Koulfoua, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar su nan take da wasu mutane 19, sannan harin ya raunata mutane 130.
Sanarwar ta mista Ban, ta bayyna harin a matsayin kisan rashin imani da kungiyar Boko Haram ke kaddamarwa.
Ban, ya bukaci kasashen da matsalar Boko Haram ta shafa, dasu binciko musabbabin bullar rikicin don daukar matakan kawo karsen sa.
Yankin gabar tafkin Chadi yana fama da hare haren kungiyar Boko Haram, lamarin da ya tilasta gwamnatin kasar Chadi kafa dokar tabaci a yankin mai makwataka da Kamaru, Nijer da kuma Najeriya.
A ranar 18 ga watan Nuwamba ne, majalisar dokokin kasar Chadi ta sake tsawaita wa'adin dokar tabacin zuwa watanni 4.(Ahmad Fagam)