in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Chadi: Shugaba Deby Itno na neman wa'adin mulki na biyar
2016-02-10 12:00:34 cri
Jam'iyyar gungun masu kishi domin ceto kasa (MPS) mai mulki ta zabi, a ranar Litinin a N'Djamena, babban birnin kasar, shugaba mai barin gado Idriss Deby Itno, a matsayin dan takararta a zaben shugaban kasa na watan Afrilun shekarar 2016 a kasar Chadi. Shugaba Deby Itno, dake kan karagar mulki tun fiye da shekaru ishirin da biyar, na neman wa'adin mulki na biyar na shekaru biyar. Zai fuskaci a gabansa wata adawa da kanta ke rabe da kuma za ta halarci zaben a warwartse. Kafin bude lokacin ajiye takardun 'yan takara a hukumar zabe mai zaman kanta (CENI), kusan manyan mutane goma ne suka riga sanar da takararsu. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China