in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Al'ummun tsibiran tafkin Chadi na matukar bukatar tallafi in ji jami'in MDD
2015-12-11 09:58:59 cri

Jami'in tsare-tsare na ofishin lura da ayyukan jin kai na MDD a yankin tafkin Chadi Stephen Tull, ya yi kira ga kasashen duniya da su taimakawa al'ummun da suka rasa matsugunnan su, sakamakon hare-haren da aka kai a tsibiran dake tafkin Chadi.

Mr. Tull, ya gabatar da wannan kira ne bayan da ya ziyarci wasu sansanoni 15 na 'yan gudun hijirar yankin. Ya ce akwai kimanin mutane 50,000 dake cikin matsanancin halin kunci na rayuwa, wanda ya hada da rashin ruwan sha da abinci, da matsugunnai, da ababen bukata na kiwon lafiya. Jami'in ya kara da cewa yanayi na fari da ke addabar yankin, ya kara tsananta halin da wadannan bayin Allah ke ciki.

Da yake tsokaci game da hare-haren da suka sabbaba wannan yanayi, Mr. Tull ya ce farmakin da aka kaiwa fararen hula, wadanda mafi yawan su manoma ne da masu su, ya yi matukar sabawa dokokin kare hakkin dan Adam da ma na kasa da kasa.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China