A cikin wata sanarwar da bangaren sojin kasar Siriya ya fidda, an ce, kwace Tadmor ya kasance wani babban koma baya ne da aka kawo wa kungiyar IS, kuma abun da zai lahanta kwarjininta, kuma za a cigaba da murkushe kungiyar IS. Sojojin gwamnatin sun kwace Tadmor, abun da ya shaida cewa, ana kan hanyar kawar kungiyar IS kwata-kwata.
Bashar ya jinjinawa taimakon da sojojin Rasha suka bayar wajen kwace tsohon garin. Ya bayyana cewa, sakamakon lalata da barnar da 'yan ta'adda suka yi, an kawo illa sosai ga tsohon garin, kuma yana fatan kasashen duniya za su tashi tsaye don shiga cikin aikin sake gina Tadmor. A sa'i daya kuma, Bashar ya jinjinawa kokarin da bangaren Rasha ya yi wajen ingiza shawarwari tsakanin bangarorin daban daban na kasar Siriya. Putin da Bashar suna fatan bangarorin daban daban na Siriya za su cimma matsaya guda da ciyar da yunkurin yin gyare-gyaren tsarin mulkin kasar gaba.(Bako)