Labarin ya bayyana cewa, kungiyar IS na ci gaba da yin garkuwa da sauran ma'aikatan kamfanin 204.
Kamfanin dillancin labarun Syria ya sanar da cewa, ba a iya yin mu'amala tare da ma'aikatan da aka yi garkuwa da su ba, yayin da bangarorin da abin ya shafa suna kokarin bincike don gano wurin da aka tsare su ciki.
Bisa labarin da gidan rediyon Sham FM na kasar Syria ya bayar a jiya, an ce, dakarun kungiyar IS sun kai hari ga wani kamfanin harhada siminti dake garin Dumayr dake dab da birnin Damascus na kasar a ranar 4 ga wannan wata, inda suka yi garkuwa da ma'aikatan kamfanin 344. (Zainab)