in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan dakarun IS dake kasar Libya ya ninka sau biyu
2016-04-08 13:36:07 cri
Kwamanda mai kula da ayyukan sojojin Amurka a nahiyar Afirka David Rodriguez, ya ce a cikin watanni 12 zuwa 18 da suka gabata, yawan dakarun kungiyar IS dake kasar Libya ya karu har ninki biyu.

Mr. Rodriguez ya bayyana a gun taron manema labaru a jiya Alhamis, cewa bisa sakon da hukumar leken asiri ta kasar Amurka ta samu, yanzu haka yawan dakarun kungiyar IS dake kasar Libya ya kai dubu 4 zuwa dubu 6, kuma yawancinsu sun shiga Libiyan ne daga Iraki, da Syria, da kuma sauran yankunan arewacin Afirka. Kaza lika akwai wasu dakaru 'yan kasar Libya, wadanda suka shiga kungiyar cikin watanni sama da 12 da suka gabata.

Rodriguez ya kara da cewa, tasirin kungiyar IS ya ci gaba da yaduwa daga babban sansaninta na Libya, da birnin Sirte dake arewacin kasar, zuwa birnin Banghazi da Derna dake arewa maso gabashin kasar, da kuma birnin Sabratha dake arewa maso yammacin kasar. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China