A wannan rana, a Geneva, mista Mistura ya ba da sanarwar cewa, a ranar 18 ga wata, kwamitin sulhu ya zartas da kudurin daidaita batun Syria ta hanyar siyasa, daga bisani, ya gaggauta kokarinsa na shiga tsakani kan batun Syria. Yana fatan kammala aikin yin shawarwari tare da jam'iyyun Syria a farkon watan Janairu na badi, daga bisani, za a kira taron yin shawarwarin wanzar da zaman lafiya tsakaninsu a ranar 25 ga watan Janairu mai zuwa a Geneva.
Ban da haka, mista Misturaya ya kalubalanci jam'iyyun kasar daban daban da su yi hadin gwiwa, su kawar da bambanci dake tsakaninsu domin kawo karshen wahalhalu da fararen hula suke sha. Dadin dadawa, ya yi kira ga kauracewa ayyukan da za su iya kawo cikas ga yunkurin siyasa, kuma ya yi kira ga kasa da kasa da su ci gaba da ba da taimako ga kasar Syria kamar yadda suke a yanzu.(Fatima)