Kakakin babban sakataren MDD Martin Nesirky ya bayyana hakan. Ya ce Mr. Ban ya gaggauta kammala ziyarar kasashen ketare, don sauraron sabon rahoto game da binciken da aka yi, don gane da zargin amfani da makamai masu guba a kasar Syria.
Ya zuwa yanzu, tawagar masu bincike kan wannan batu ta MDD ta riga ta kammala ayyukanta, kuma za ta tashi daga birnin Damascus a yau Asabar 31 ga wata. Kakakin babban sakataren MDD ya kuma jadadda cewa, za a tsaida shawara kan wannan batun bayan kammala cikakken nazari kan samfurin sinadarai da tawagar binciken ta samo a kasar ta Siriya.
Bugu da kari, bisa labarin da aka samu a ran Juma'a 30 ga wata, babbar wakiliya mai kula da harkokin soja ta MDD Angela Kane, ta tashi daga kasar Syria zuwa Turkiya. A kuma ran 29 ga wata, kakakin mataimakin babban sakataren MDD ya bayyana cewa, hakan ba shi da nasaba da rade-radin da ake yi cewa kila kasashen yammacin Turai za su yi kawancen daukar matakan soja kan gwamnatin ta Siriya. (Maryam)