Kudurin ya nanata cewa, kwamitin sulhu ya amince da sanarwar Geneva da aka fitar a shekarar 2012 da matsaya daya da aka cimma a gun taron ministocin harkokin waje karo na biyu kan batun Syria da aka yi a watan Nuwamban bana, kuma ya jaddada cewa, jama'ar Syria za su yanke shawarar makomar kasar. Kwamitin sulhun ya bukaci babban sakataren MDD da ya kira jam'iyyun adawa da gwamnatin Syria da su yi shawarwari a tsakaninsu a hukunce kan yunkurin siyasa na rikon kwarya bisa wadannan bayanai biyu. Ana sa ran cewa, za su yi shawarwarin a farkon watan Janairun badi, da zummar daidaita batun Syria ta hanyar siyasa.
Kudurin ya ce, kwamitin sulhu ya nuna goyon baya ga tsagaita bude wuta a duk fadin kasar Syria, kuma ya bukaci bangarorin da su daina kai hari kan fararen hula nan take. Ya yi kira ga bangarorin da su samar da wata hanyar mu'amala ga hukumomin agajin jin kai.
Ban da haka kuma, kwamitin sulhu ya sake yin kira ga kasa da kasa da su yin rigakafi da yaki da ayyukan ta'addanci da kungiyar IS da ta Al-Nusra front, da sauran mutane da kungiyoyin dake da alaka da kungiyar Al-Qaeda suke yi, bisa kudurin da kwamitin sulhun MDD ya zartas da shi.(Fatima)