in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya za ta aiwatar da kasafin kudinta na 2016
2016-04-08 11:00:46 cri

A ranar Alhamis din da ta gabata ne, gwamnatin kasar Najeriya ta sha alwashin aiwatar da kasafin kudin kasar na shekarar 2016 bi da bi, don tabbatar da bunkasar ci gaban kasar.

Yayin taron manema labarai a birnin Abuja, ministan kasafin kudi da tsare-tsaren kasa na Najeriyar Udoma Udo Udoma ya ce, gwamnatin kasar ta tsara wani jadawali da zai taimaka wajen samun nasarar aiwatar da kasafin kudin kasar daki-daki.

A cewarsa, gwamnatin ta tsara hakan ne domin tabbatar da ganin an sarrafa kudaden yadda ya kamata don gina tattalin arzikin kasar.

Game da manyan ayyuka dake kunshe a kasafin kudin kasar, ministan ya ce, an yi tanadi na musamman domin ganin an fitar da kudaden bisa ka'ida da kuma amfani da su kamar yadda aka tsara.

Ya ce, kunshin kasafin kudin kasar ya yi wani tanadi na musamman game da takaita shigo da kayayyaki daga kasashen ketare da bunkasa fitar da kayayyakin kasar zuwa kasashen waje.

A ranar 23 ga watan Maris ne, majalisar dokokin kasar ta amince da kasafin kudin wanda fadar shugaban Najeriyar ta aike da shi tun a watan Disambar shekarar da ta gabata, amma sai a jiya Alhamis ne aka gabatar wa ofishin shugaban Najeriyar cikakkun bayanai game da kunshin kasafin kudin kasar.

Tun da farko, shugaba Muhammadu Buhari na Najeriyar ya ambata cewar, zai sake yin bitar kasafin kudin kasar a tsanake wanda yawansa ya tasamma dalar Amurka biliyan 30.(Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China