Hukumar 'yan sandan kasar Najeriya a jiya Talata ta ayyana ci gaba da yaki da masu yin garkuwa da mutane a jihar Kaduna dake shiyyar arewacin kasar.
Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Kaduna Zubairu Abubakar, ya sheda wa kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua cewar, tuni hukumar ta kafa wata tawaga don yin farautar masu aikata mugun laifukan yin garkuwa da mutane a sassan jihar.
Ya ce, hukumar ta dauki wannan mataki ne bisa samun umarni daga babban sifeton 'yan sandan kasar Solomon Arase.
Mutane masu yawa ne aka yi garkuwa da su don neman kudaden fansa a garuruwa da kauyuka a kananan hukumomin jihar Kaduna 23 cikin watanni 3 da suka gabata.
Na baya-bayan nan shi ne wani kanal a rundunar sojan kasar wanda aka tsinci gawarsa bayan yin garkuwa da shi a ranar 25 ga wata Maris. (Ahmad)