in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta ce babu sauran yanki a hannun Boko Haram a arewa maso gabashin kasar
2016-03-31 10:35:20 cri
A jiya Laraba gwamnatin Najeriya ta musanta rahotannin da wasu shafukan yanar gizo ta Internet ke yadawa na cewar har yanzu mayakan Boko Haram na rike da ikon kananan hukumomi a arewa maso gabashin kasar.

Ministan tsaron kasar birgediya janar Mansur Dan-Ali mai ritaya, ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa ga kamafanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua a Abuja.

Ministan ya karyata rahoton, da kuma wani rahoton dake cewa an mai da 'yan matan sakandaren Chibok da aka yi garkuwa dasu shekaru biyu da suka gabata suka zama 'yan kunar bakin wake

Ministan ya ce an sauya ainihin kalaman da ya furta a shafukan Internet din.

Dan Ali, cikin wata hira ta musamman da sashen Hausa na muryar Amurka, ya yi jawabi ne game da irin nasarorin da sojojin kasar ke samu a yaki da ta'addanci a shiyyar arewa maso gabashin kasar.

Ya ce kafin wannan lokaci, sama da kananan hukumomi 60 ke karkashin ikon mayakan na Boko Haram, amma a halin yanzu, an murkushe su baki daya, sai kananan hukumomi ne 2 tak ake duriyar mayakan na Boko Haram, amma duk da haka, ba su ne ke rike da ikon a kananan hukumomin biyu ba.

Game da 'yan matan Chibok, ministan ya ce baya nufin na sakandaren Chibok da aka sace a ranar 14 ga watan Aprilun 2014, sai dai yana nufin yara mata da aka yi garkuwa da su a kananan hukumomin dake yankin.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China