Vincent Olatunji, shi ne mai rikon mukamin daraktan cibiyar bunkasa fasahar sadarwa na kasar NITDA, ya tabbatar da hakan a Abuja cewar, daga cikin adadin kimanin laifukan 2,500 ne aka yi nasarar aiwatar da su yayin da aka dakile saura.
Ya kara da cewar ana samun karuwar amfani da hanyoyin yanar gizo a kasar.
A cewarsa, sama da mutane miliyan 90 ne ke ta'ammali da yanar gizo a kasar a kullum, wajen harkokin kasuwanci na biliyoyin kudade.
Vincent, ya tabbatar da cewar, hukumar za ta ci gaba da iyakar kokarinta wajen bada kariya a fannin yanar gizo.(Ahmad)