Pinnick, ya fada a taron manema labarai a Abuja cewar, wanan abu tsautsayi ne, kasancewar kungiyar wasan ta yi iyakar kokarinta amma ba ta kai ga nasara ba.
Ya ce NFF zata mai da hankali, domin kungiyar ta samu shiga gasar share fagen na cin kofin duniya a 2018 wanda za'a buga wasan karshe a kasar Rasha.
NFF ta nuna farin ciki, kasancewar kungiyar Super Eagles na daga cikin wadanda ke da damar shiga gasar ta ta 2018.
Yanzu haka dai, kasar Masar ta samu nasarar shiga gasar ta 2017 a kasar Gabon, bayan da ta doke Najeriyar da ci 1 da nema.(Ahmad Fagam)