Babban kwamandan rundunar tsaron jama'a na kasar Abdullahi Gana ya tabbatar da hakan, ya ce, hukumar ta dauki wannan mataki ne domin maye gurbin jami'an tsaron da suka rasu a yayin da suke bakin daga a yankunan kasar domin tabbatar da tsaro.
Ya kara da cewa, wannan shiri ya hada da tura jami'an 'yan sanda kimanin dubu 6 a yankunan shiyyar arewa maso gabashin kasar domin ci gaba da murkushe mayakan Boko Haram.
Ya ce wannan yunkuri da hukumar ta NSCDC ta yi, zai taimakawa kokarin da jami'an 'yan sandan kasar ke yi na wanzar da tsaro a yankunan kasar. (Ahmad Fagam)